Isa ga babban shafi
China

Yawan al'ummar China ya ragu a cikin shekaru 70

A karon farko cikin shekaru 70 da suka gabata, yawan al’ummar China ya ragu kamar yadda kwararru suka bayyana, amma sun yi gargadin cewa, karancin matasa zai yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin kasar.

Wani yanki na al'ummar China
Wani yanki na al'ummar China Reuters
Talla

China wadda ta zarce kowacce kasa wajen yawan al’ummar da adadinta ya kai miliyan dubu 1 da miliyan 400, ta kafa dokar haihuwar yaro ko kuma yarinya guda, tsarin da ake ganin zai kare karfin tattalin arzikin kasar.

Sai dai a shekarar 2016, kasar ta sauya wannan doka, in da ta amince wa ma’aurata da su haifi yara biyu kacal bayan ta nuna fargaba kan cewa, tsofaffi za su mamaye kasar baki daya, abin da zai tauye adadin ma’aikata matasa masu jini a jika.

A shekarar 2018 da ta gabata, kididdigar haihuwar jarirai a dukkanin fadin kasar ta ragu da miliyan 2 da dubu 500 , abin da ya saba da hasashen da kwararru suka yi na cewa, yawan al’ummar kasar zai karu da sabbin jarirai dubu 790 a shekarar ta bara.

Tun bayan da China ta samar da tsarin takaita haihuwar yaro guda a shekarar 1979, ba a samu yawan haihuwa ba kamar yadda aka yi ta hasashe duk da cewa, daga bisani an kara bai wa ma’aurata damar haihuwar yara biyu.

Yanzu haka dai, ana ganin da yiwuwar gwamnatin kasar ta kara sassauta dokar haihuwar a China, amma kuma, da dama daga cikin ma’aurata na gudun haihuwar yara da yawa saboda tsadar karatun boko da kudin asibiti da kuma kudin hayar gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.