Isa ga babban shafi
Bangladesh

Hasina ta lashe zaben Bangladesh da gagarumin rinjaye

Hukumar zaben Bangladesh ta ce Fira Minista Shiekh Hasina, ta lashe babban zaben kasar da gagarumin rinjaye, nasarar da ta bata damar zarcewa zuwa shugabancin kasar wa’adi na hudu a jere.

Fira Ministar Bangladesh Sheikh Hasina tare da magoya bayanta a birnin Dhaka. 30/12/2018.
Fira Ministar Bangladesh Sheikh Hasina tare da magoya bayanta a birnin Dhaka. 30/12/2018. Bangladesh Sangbad Sangstha/Handout via REUTERS
Talla

Sai dai ‘yan adawa suka yi fatali da sakamakon, tare da bukatar a sake sabon zabe, saboda a cewar su, an tafka magudi hadi da cin zarafin magoya bayansu.

Yayin da yake sanar da sakamakon, sakataren hukumar zaben kasar Helal Uddin Ahmed ya ce jam’iyyar Awami League ta Fira Minista Hasina da sauran masu kawance da ita, sun lashe kujeru 288 na majalisar kasar daga cikin kujeru 300, yayinda babbar jam’iyyar adawa ta BNP ta samu kujeru 6 kacal.

Duk da zaben na jiya ya gudana cikin tsauraran matakan tsaro inda jami’an ‘yan sanda dana soji dubu 600 ke sintiri, sai da rayukan mutane 17 suka salwanta, sakamakon arrangama tsakanin magoya bayan jam’iyyar Awami mai mulki da kuma ta BNP.

Hakan yasa jagoran gamayyar ‘yan adawa Kamal Hossain kiran a sake sabon zabe, bisa zargin tafka magudi da cin zarafin magoya bayansu.

Duk da cewa an yabawa Fira Minista Hasina kan farfado da tattalin arzikin kasar, da kuma tallafawa dubban 'yan gudun hijirar kabilar Rohingya, kungiyoyin kare hakkin dan adam na zarginta da tsare dubban magoya bayan babbar abokiyar hamayyarta Khaleda Zia jagorar BNP, wadda yanzu haka ke karkashin hukuncin zaman gidan yari na shekaru 17, kan zargin cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.