Isa ga babban shafi
Syria

Turkiya ta sha alwashin karbar jagorancin yaki da IS a Syria

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya ce kasar za ta karbi jagorancin yakar mayakan IS da ke Syria, idan Amurka ta janye dakarunta daga kasar.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan. REUTERS/Umit Bektas
Talla

Alwashin na shugaban na Turkiya a ranar Juma'a, ya zo kwanaki biyu bayan da acikin yanayi na bazata shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirin janye dakarunsa 2000 da ke Syria da ke taimakawa mayakan Kurdawa, bayan ikirarin nasara a yaki da IS da ya ce sun samu.

Turkiya ta yi maraba da matakin na Amurka, la'akari da cewa zai kawo karshen goyon bayan da mayakan Kurdawa na YPG ke samu daga gareta a Syria, musamman a arewacin kasar.

Turkiya dai na kallon Kurdawan na YPG a matsayin ‘yan ta’adda kuma reshen haramtacciyar kungiyar Kurdawan kasar ta PKK da ke fafutukar ballewa daga cikinta domin kafa kasar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.