Kurdawan Syria sun nemi ceton Faransa daga farmakin Turkiya
Kurdawan kasar Syria sun bukaci Faransa da ta basu taimakon gaggawa na diflomasiya da soji, domin kare kansu ga barazanar fuskantar farmakin sojin kasar Turkiya.
Wallafawa ranar:
Neman agajin da mayakan Kurdawan na kungiyar YPG, na zuwa ne bayan da a ranar Laraba, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirin janye dakarunsa da ke baiwa Kurdawan gowon baya wajen yakar kungiyar ISIS a arewacin Syria
Janyewar sojin Amurka daga Siriya na iya haifar da tsaiko ga kokain murkushe mayakan ISIS da Kurdawan ke yi.
A halin yanzu dai akalla dakarun Amurka 2000 ke cikin Syria, wadanda ke taimakawa mayakan Kurdawa na YPG wajen yakar kungiyar ISIS, sai dai Turkiyya na kallon su a matsayin ‘yan ta’adda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu