Isa ga babban shafi
Yemen

An soma taron sasanta rikicin kasar Yemen

Yau ake soma taron sasanta rikicin kasar Yemen a Sweden wanda zai kunshi wakilan ‘Yan Tawayen Houthi da na gwamnati, domin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 4 ana fafatawa.

Wasu kananan yara dake cin biredi a sansanin 'yan gudun hijira dake gaf da birinin Aden, wadanda suka tsere daga birnin Hodeidah. 12/11/2018.
Wasu kananan yara dake cin biredi a sansanin 'yan gudun hijira dake gaf da birinin Aden, wadanda suka tsere daga birnin Hodeidah. 12/11/2018. REUTERS/Fawaz Salman
Talla

Taron, wanda zai gudana a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, shi ne irin sa na farko tun shekarar 2016 lokacin da wani yunkurin gudanar da makamancinsa ya ruguje.

Majiyar Majalisar Dinkin Duniya tace matakin farko a taron, shi ne na ganin wakilan bangarorin biyu sun amince da juna kafin soma tattaunawa matsalolin da suka addabi kasar.

Yakin da aka shafe shekaru 4 ana gwabzawa tsakanin ‘yan tawayen Houthi da rundunar hadin gwiwa ta wasu kasashen larabawa da Saudiya ke jagoranta, ya lakume rayukan mutane akalla 100,000, tare da kuma jefa mutane miliyan 14 cikin bala’in yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.