Kakakin Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Joel Millman, ya sheidawa manema labarai a Geneva cewar, yanzu haka kasar Yemen ta kasance babbar hanya da ‘yan gudun hijirar Afirka ke amfani don isa wadatattun kasashen yankin Gulf.
Joel ya ce, masu safarar mutane na amfana da yakin kasar wajen kaucewa shingayen binciken jami’an tsaro, don shiga kasar.
Millman ya ce, kwararan ‘yan gudun hijira zuwa Yeman zai karu da kashi hamsin, a wannan shekara, ma’ana karin dubu hamsin kan dubu 100 da suka shiga kasar a bara.
Yaki tsakanin ‘yan tawayen houti da dakarun gwamnati da ke samun goyan bayan kasashen kawance da Saudiya ke jagoranta a Yemen ya hallaka mutane da dama tare da haddasa talauci a kasar,.