Isa ga babban shafi
Qatar

Qatar za ta fice daga kungiyar OPEC

Gwamnatin Qatar ta yanke shawarar janye kasar daga cikin kungiyar OPEC mai kunshe da kasashe masu arzikin danyen man fetur.

Saad al-Kaabi, Ministan albarkatun mai da sauran makamashi na kasar Qatar, yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Doha. 4/7/2017.
Saad al-Kaabi, Ministan albarkatun mai da sauran makamashi na kasar Qatar, yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Doha. 4/7/2017. Naseem Zeitoon/ REUTERS
Talla

Sanawar ta bazata da ministan makamashin Qatar Sa’ad Sherida al-Ka’abi ya bayyana, na nuni da cewar, kasar na son cimma burinta na kara yawan gangar danyen man da take haka, domin karfafa tattalin arzikinta dake fuskantar kalubale a dalilin yanke huldar da Saudiya ta yi da ita, tare da goyon bayan kasashen Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Baharain.

Karo na farko kenan da wata kasa ta Yankin Gabas ta Tsakiya ke ficewa daga cikin kungiyar ta OPEC wadda aka kafa a shekarar 1960.

Yayin sanar da daukar matakin Ministan makamashin Qatar al-Ka’abi ya ce kasar za ta kara yawan gangar danyen man da take hakowa daga gannga miliyan 4 da dubu 800 a rana guda zuwa ganga miliyan shidda da rabi.

A bangaren Iskar Gas kuwa, ministan ya ce Qatar za ta kara yawan wadda take hakowa daga ton miliyan 77 a kowace shekara zuwa ton miliyan 110.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.