Kungiyar Amnesty International da ke da Cibiya a London ta ce ta janye lambar girmar da aka bai wa Aung San Suu Kyi a shekarar 2009 lokacin da sojoji ke tsare da ita ya zama wajibi, sakamakon yadda ta shafawa idanun ta toka lokacin da ake cin zarafin Yan kabilar Rohingya.
Kumi Naidoo, shugaban kungiyar ya ce a yau suna nadamar cewar Suu Kyi ba za ta iya wakiltar muradun kungiyar ba da kuma kare hakkin Bil Adama, saboda haka Amnesty ba za ta iya kare dalilan da za su sa Suu Kyi ta cigaba da rike lambar girmar ba.
Naidoo ya ce tun a ranar lahadi sun sanar da ita matsayin su na cire mata lambar girmar, kuma ya zuwa yanzu ba ta ce komi akai ba.
Wannan ba shine karo na farko da ake karbe lambar girmar da aka bai wa Suu Kyi ba, saboda cin zarafin da ake yi wa Musulmin kasar ta Myanmar.