Isa ga babban shafi
Syria

Sojin Syria sun hallaka 'yan tawaye 23 a lardin Idlib

Kungiyar Syrian Observatory dake sa ido kan yakin Syria, tace sojojin kasar sun hallaka mayakan ‘yan tawaye 23, a wani farmaki da suka kai musu a gaf da lardin Idlib.

Yankin kewayen lardin Idlib da sojin Syria suka kaiwa 'yan tawaye farmaki mai makwabtaka da lardin Hama.
Yankin kewayen lardin Idlib da sojin Syria suka kaiwa 'yan tawaye farmaki mai makwabtaka da lardin Hama. AFP
Talla

Inda aka kai harin na baya bayan nan, yana cikin yankunan kewayen lardin na Idlib da aka cimma yarjejeniyar haramta kai hari cikinsa, tsakanin Rasha da Turkiya.

Mayakan da sojin na Syria suka hallaka a kan iyakar arewa maso yammacin lardin na Idlib, na biyayya ne ga wata kungiyar ‘yan tawaye mai masa sunan Jaish al-Izza.

Tun bayan cimma yarjejeniyar haramta kai hari a lardin na Idib da kewayensa an samu rahotannin karya yarjejeniyar a lokuta da dama, sai dai harin baya bayan nan shi ne mafi muni, wanda aka hallaka ‘yan tawaye 23 da jikkata wasunsu 35.

Lardin Idlib shi ne yanki na karshe mafi girma dake hannun ‘yan tawayen Syria, inda kungiyoyin agaji sukai gargadin cewa kaddamar da farmaki da nufin murkushe su, zai iya haifar da tagayyarar fararen hula mafi muni da aka taba gani tun bayan barkewar yakin basasar kasar ta Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.