Isa ga babban shafi
Indonesia

Indonesia: Ana kukan targade karaya ta samu

Jami’an agaji a Indonesia na gudanar da aikin ceto kashi na karshe a garin Palu dake tsibirin Sulawesi, inda girgizar kasa mai karfin maki 7.5 ta afkawa a ranar 28 ga watan Satumban da ya gabata.

Wani yankin tsibirin Sulawesi da girgizar kasa ta afkawa.
Wani yankin tsibirin Sulawesi da girgizar kasa ta afkawa. JEWEL SAMAD / AFP
Talla

Akalla jami’an agaji dubu 10 ne ke gudanar da aikin ceton, tare da fatan zakulo wadanda sukai saura da rai daga karkashin baraguzan ginin da suka danne su, sai kuma gawarwakin wadanda suka rasa rayukansu a dalilin girgizar kasar.

Alkalumman da jami’an agajin a kasar ta Indonesia suka fitar sun nuna cewa, mutane dubu 2 da 45 ne suka hallaka a girgizar kasar ta karshen watan Satumba, yayinda har yanzu aka kasa gano mutane akalla dubu biyar da suka bace.

Masu azancin magana na cewa “ana kukan targade karaya ta samu”, domin kuwa, a dai dai lokacin da dubban jami’an agaji ke kokarin aikin ceto a kasar ta Indonesia, wata sabuwar girgizar kasar ta afkawa tsibiran Bali da kuma Java, inda ta hallaka mutane uku a Java, tare da rusa gine-gine da dama.

Girgizar kasar ta wannan Alhamis, ta afkawa tsibirin Bali ne, a daidai lokacin da tsibirin ke karbar bakuncin, manyan jami’an kasashen duniya da sauran masu ruwa da tsaki, akalla dubu 19, ke halartar taron hadin gwiwa tsakanin asusun bada lamuni na duniya, da kuma bankin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.