Isa ga babban shafi
Syria

Syria ta yi afuwa ga dubban sojin da suka tserewa filin daga

Shugaban Syria Bashar Al-Assad ya sanar da yin afuwa ga dukkanin sojin kasar da suka bijire wa gwamnati tare da tserewa daga bakin aiki, yayinda kasar ke fama da yakin basasa.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad.
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad. SANA/Handout via REUTERS
Talla

Assad ya kuma yi afuwa ga dubban matasa masu jini a jika da suka ki shiga ayyukan soji da gwamnati ta wajabta musu bayan barkewar yakin da kasar ke fama da shi tsawon shekaru 7.

Wasu daga cikin dubban sojin Syrian da suka tsere bayan barkewar yakin kasar a 2011, sun shiga kungiyoyin ‘yan tawaye, wasu kuwa suka boye a gidajen su, yayin da wasu suka tsere zuwa kasashen waje.

A bangaren matasa masu jini a jika kuwa, tsoron kada a tura su filin daga ne ya sa mafi akasarin matasan Syria, dake gudun hijira suka bijirewa komawa kasarsu.

Gwamnatin Syria, ta bukaci wadanda suka tsere dasu gabatar da kansu ga hukumomin kasar nan da watanni 4, yayinda aka baiwa wadanda suka tsere daga kasar watanni 6 su dawo bayan afuwar da aka yi musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.