Isa ga babban shafi
Indonesia

Girgizar kasa ta hallaka mutane kusan 1000 a Indonesia

Mahukuntan Indonesia sun bukaci gudanar da jana’izar bai-daya cikin gaggawa don kaucewa yaduwar cututuka sakamakon tarin gawarwakin mutane sama da 1000 da aka jibge, biyo bayan ibtila’in girgizar kasa da ta rutsa da su.

Ibtila’in girgizar kasa da ta rutsa da jama'a a Indonesia
Ibtila’in girgizar kasa da ta rutsa da jama'a a Indonesia Antara Foto/Rolex Malaha via REUTERS
Talla

Mahukunatn Indonesia sun gargadi cewa, akwai yiwuwar tashin alkaluman mamatan zuwa dubbai, lura da cewa, har yanzu ana ci gaba da aikin zakulo wadanda suka makale a birnin Palu, yayin da ‘yan uwa da abokan arziki ke share wuraren-wucen gadi don ajiye gawarwakin masoyan su.

Masu aikin agaji a tsibirin Sulawesi sun shafe tsawon sa’oi na ceton mutanen da har yanzu ke makale a cikin buraguzai saboda rashin kayan aiki.

Rahotanni na cewa, ana jin sautukan jama’a ciki har da kukan wani jariri da suka makale a buraguzan wani otel da suka danne su.

Wadanda suka tsallake rijiya da baya a wannan ibtila’in na girgizar kasa da ambaliyar ruwan tsunami a Indonesia, sun koma fasa shaguna don kwashe kayayyakin abinci da ruwasn sha,

kuma jami’an ‘yan sanda sun zura musu ido ba tare da tsawatar musu ba.

Tuni shugaban kasar, Joko Widodo ya ziyarci yankin, in da ya zaburar da jama’a da su ci gaba da aikin agaji.

Hukumar Kul ba Aukuwar Bala’oi ta Indonesia ta ce, za a samu karin mutanen da lamarin ya shafa kuma tuni ta sanar da gudanar da jana’izar bai-daya don dakile yaduwar cututuka tsakanin al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.