Isa ga babban shafi
India

Lalata da matar wani ba laifi ba ne a India- Kotu

Babbar kotun India a yau Alhamis, ta yanke hukuncin cewa aikata laifin cin amanar ma’aurata ko kwartanci ba laifi bane a kasar.

Harabar kotun kolin kasar India.
Harabar kotun kolin kasar India. DNA India
Talla

Yayin da take yanke hukuncin soke dokar da India ta shafe sama da shekaru 100 tana aiki da ita, babbar kotun kasar ta ce zartas da hukuncin dauri akan wadanda aka samu da laifin cin amanar abokan zamansu na aure cin zarafin dan adam ne.

A cewar kotun dokar ta baya da aka kafa a zamanin mulkin mallaka, ta tauye mata hakkinsu na ra’ayi ko zabin da ya shafi rayuwarsu, zalika haramtawa matan aure ko magidanta neman wasu ma’auratan da lalata, tamkar mayarda mata dukiya ko kadara ce ga maza.

A karshe babbar kotun ta India ta fayyace cewa matakin cin amanar juna da ma’aurata kan yi da ake kallo a matsayin laifi a baya, a halin yanzu ba laifi bane illa zabi na abinda ya shafi rayuwar dan adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.