Isa ga babban shafi
India

Mabiya addinin Hindu 50 sun mutu a hadarin mota a India

Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu bayan da wata mota dauke da mutane 80 a hanyarsu ta dawowa daga wani wurin ibada ta kwace wa direbanta sannan ta fada a wani rafi da ke gefen hanya a kasar India.

Rahotanni sun ce fiye da rabin mutanen da suka mutu a hadarin mata ne sai kuma wasu kananan yara 3.
Rahotanni sun ce fiye da rabin mutanen da suka mutu a hadarin mata ne sai kuma wasu kananan yara 3. Fuente: Reuters.
Talla

Mutanen sun dawo ne daga wurin ibadar Hindu da ake kira Kondagattu Anjaneya Swamy, da ke kudancin jihar Telanga to sai dai an kaddamar da bincike domin gano musabbabin faruwar hadarin.

Kusan kowacce shekara mutane dubu 150 ke rasa rayukansu sanadiyyar hadarin mota a India wanda ake alakantawa da rashin kyawun hanyoyi ko kuma a wasu lokutan rashin lafiyar ababen hawa yayinda wani lokacin ke zamowa tukin ganganci.

Rahotanni sun ce fiye da rabin mutanen da suka mutu a hadarin mata ne sai kuma wasu kananan yara 3.

Mabiya addinin Hindu dai na daukar ranar ta yau mai matukar muhimmanci da ke tattare da alkhairi dalilan da ya sa kusan ko'ina mabiyan suka fito don gudanar Ibadu a wuraren bauta.

Ministan jihar ta Telanga Chandrashekhar Rao ya sanar da bayar da rupee dubu dari biyar dai dai da dalar Amurka dubu bakwai ga kowanne iyalan mamata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.