Isa ga babban shafi
Japan

Guguwa mai karfi ta afka wa Japan

Kasar Japan ta gamu da ibtila’in guguwa mafi muni cikin shekaru 25, abin da ya sa hukumomi suka gargadi mutane sama da miliyan daya da su fice daga gidajensu bayan mutuwar mutane akalla biyu.

Guguwar mai dauke da iska da ruwan sama ta yi barna musamman a kudancin Japan
Guguwar mai dauke da iska da ruwan sama ta yi barna musamman a kudancin Japan Mandatory credit Kyodo/via REUTERS
Talla

Guguwar wadda aka yi wa lakabi da Jebi da kuma ke dauke da iska mai hade da ruwan sama, ta yi matukar barna musamman a yankin kudancin kasar.

An ga yadda guguwar ta yi fatali da wata katuwar tankar mota, yayin da ta babbako da rufin ginin tashar jiragen kasa ta Kyoto.

Ana fargabar ibtila’in ka iya haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar laka bayan ya katse wutar lantarki na gidajen dubban jama’a.

Kazalika an soke zirga-zirgar jiragen kasa da na sama har ma da na ruwa a sanadiyar guguwar.

Kawo yanzu babu rahoto game da jumullar adadin mutanen da gaguwar ta yi wa illa, yayin da ake sa ran sassaucinta nan da wani lokaci duk da cewa tana ci gaba da karade sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.