Dakarun Rasha dake Syria sun kara kwarewa a fagen yaki
Rasha ta ce dakarunta dubu 63 ne ke Syria domin fada da ayyukan ta’addanci, kuma hakan ya ba su damar kara gogewa a fagen daga.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce daga cikin wannan adadi, dubu 25 da 738 kananan sojoji ne, sai masu rike da mukamin janar su 434, yayin da sauran dubu 4 da 339 ke da kwarewa ta fannin sarrafa manyan makamai da kuma harba rokoki.
A dai gefen kuma, Jagoran daya daga cikin kungiyoyin da ke ikirarin jihadi a Syria, ya gargadi kungiyoyin ‘yan tawaye da ke yankin Idlib, da su guji shiga tattaunawa da gwamnatin Bashar Assad.
Shugaban kungiyar Hayat Tahrir al-Sham Abu Mohamed Al-jolani, ya yi wannan gargadi ne bayan da Bashar Assad ya bayyana cewa, a shirya dakarunsa suke su karbe ikon wannan lardi da ke kusa da iyakar kasar da Turkiyya, to sai dai Assad ya yi tayin shiga tattaunawa da wadanda ke son ajiye makamansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu