Isa ga babban shafi
India

Yawan wadanda suka mutu a ambaliyar ruwan Kerala ya haura 350

Yawan wadanda suka hallaka a ambaliyar ruwa mafi muni da ta afkawa jihar Kerala da ke kudancin India ya karu zuwa mutane 357, a dai dai lokacin da masu hasashen yanayi sukai gargadin za'a ci gaba da fuskantar saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar.

wasu daga cikin jami'an agaji yayin aikin ceto mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa su a yankin Aluva da ke kudancin jihar Kerala a kasar India.
wasu daga cikin jami'an agaji yayin aikin ceto mutanen da ambaliyar ruwa ta rutsa su a yankin Aluva da ke kudancin jihar Kerala a kasar India. REUTERS/Sivaram V
Talla

Tuni dai gwamnatin India ta yi shelar cewa jihar ta Kerala, na fuskantar ambaliyar ruwa mafi muni da aka taba gani cikin shekaru akalla 100.

Tun bayan fara saukar ruwan sama mai karfi da ya haddasa ambaliya da zaftarewar kasa, daga ranar 8 ga watan Agusta zuwa yau, sama da mutane 300,000 sun rasa muhallansu, sakamakon yadda ambaliyar ta mamaye akalla kauyuka 2,600.

Bayaga dubban gidajen da ta rusa, ambaliyar ta lalata manyan hanyoyin da aka kiyasta tsawonsu ya haura kilomita 10,000.

Sakamakon wata kididdiga da jami'an kasar ta India suka yi a baya bayan nan, ya nuna cewa dukiyar da ta salwanta sakamakon ambaliyar ruwan ta jihar Kerala ta kai darajar akalla dala biliyan 3.

Jami'an agaji na ci gaba da fuskantar kalubalen aikin ceton da suke, sakamakon hanyoyin sada sassan jihar akalla 134 da suka yanke lamarin da ya haifar da wahalar isa kan tsaunuka ko tuddan da wasu tarin jama'a ke zaune.

Zuwa yanzu gwamnati da hadin gwiwar kungiyoyin agaji sun kafa sansanoni dubu 3,026 domin baiwa wadanda ambaliyar ta raba da muhallansu mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.