Isa ga babban shafi
Qatar

Qatar ta zargi Saudiya da haramtawa 'yan kasarta aikin Hajji

Qatar da zargi Saudiya da hana ‘yan kasarta damar gudanar da ibadar aikin hajjin bana, zargin da Saudiya ta musanta.

Al'ummar Musulmi yayin gudanar da Ibada a Masallacin Makkah.
Al'ummar Musulmi yayin gudanar da Ibada a Masallacin Makkah. REUTERS/Suhaib Salem
Talla

Tun bayan tsamin dangantakar da ta shiga tsakanin kasashen biyu, Saudiya ta haramtawa ‘yan kasar Qatar shiga cikinta, to sai dai gwamnatin Saudiyan ta ce haramcin bai shafi lokacin aikin Ibada na Hajji ba.

Akalla ‘yan kasar Qatar 1,200 Saudiya ta baiwa damar gudanar da aikin Hajjin na bana a karkashin tsarin adadin da gwamnatin Saudiyan ke warewa kowace kasa.

Tun a watan Yuni da ya gabata ne, ma’aikatar lura da gudanar aikin hajji ta Saudiya, ta sanar da bude wani shafin Internet da zai baiwa ‘yan Qatar damar rijistar shiga aikin hajjin bana, to sai dai a baya bayan nan ‘yan kasar ta Qatar sun koka bisa gaza samun damar yin rijistar.

A watan Yunin shekarar 2017, Saudiya, hadaddiyar daular larabawa, Bahrain da Masar suka yanke duk wata alaka tsakaninsu da Qatar, tare da rufe iyakokinsu da ta sama kasa da kuma ruwa, duk saboda zarginta da marawa wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.