Isa ga babban shafi
India-Ambaliya

Mutanen da suka mutu a Ambaliyar ruwan India sun kai 324

Gwamnatin India ta sanar da cewa adadin wadanda da suka mutu a ambaliyar ruwan jihar Kerala ya karu zuwa mutane 324. Wani sako da Ministan jihar Pinarayi Vijayan ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce ambaliyar ita ce mafi muni da India ta fuskanta cikin shekaru 100 da suka gabata.

Fiye da jiragen Shalkwafta 30 tare da jiragen ruwa 320 ne yanzu haka ke ci gaba da aikin ceto don gano daruruwan jama’ar da suka bace tare da tseratar da masu sauran lumfashi.
Fiye da jiragen Shalkwafta 30 tare da jiragen ruwa 320 ne yanzu haka ke ci gaba da aikin ceto don gano daruruwan jama’ar da suka bace tare da tseratar da masu sauran lumfashi. REUTERS/Sivaram V
Talla

Ambaliyar wadda aka shafe kwanaki 10 ana yi a jihar ta Kerala mai yawan ‘yan yawon bude ido baya ga kisan tarin jama’ar ta kuma lalata dimbin duniya tare da tilastawa miliyoyin jama’a kauracewa muhallansu.

Rahotanni sun ce cikin kasa da sa’o’i 24 da suka gabata ne Ambaliyar ruwan ta tsananta zuwa zaftarewar laka yayinda ta lalata tarin gidaje.

Fiye da jiragen Shalkwafta 30 tare da jiragen ruwa 320 ne yanzu haka ke ci gaba da aikin ceto don gano daruruwan jama’ar da suka bace tare da tseratar da masu sauran lumfashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.