Isa ga babban shafi
Korea

Kasashen Koriya za su gudanar da taron hadin-kai

Kasashen Koriya sun yanke shawarar gudanar da wani taro a cikin watan Satumba mai zuwa a birnin Pyongyang na Koriya ta Arewa, da zai zama wani sabon mataki mai matukar muhimmanci a kokarinsu na kara samun hadin-kai a tsakaninsu.

Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un da takwaransa na Koriya ta Kudu, Moon Jae In
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un da takwaransa na Koriya ta Kudu, Moon Jae In The Presidential Blue House /Handout via REUTERS
Talla

Wannan labari ya fito ne a cikin wata sanarwa ta hadin guiwar kasashen da aka yada a daura da zaman taron tattaunawa da bangarorin biyu ke yi a yankin iyakokinsu.

Ziyarar da shugaba Moon Jae-in zai kai birnin Pyongyang, za ta kasance irinta ta farko da wani shugaban Koriya ta Kudu ya kai a tsawon shekaru sama da 60.

Sai dai duk da cewa, kasashen biyu na kara kusantar juna, takunkuman da kasashen duniya suka kakaba wa Koriya ta Arewa saboda ayyukanta na nukliya, sun hana sake maido da huldar cinikayya da ta tattalin ariziki tsakanin kasashen biyu, duk cewa Koriya ta Arewar ta nuna aniyarta karara ta kwance damarar makamanta na nukiliya.M

Masharhanta na ganin taro na watan Satumba zai iya zama wata dabara daga Koriya ta Arewa domin samun damar ci gaba da tattaunawa da kasar Amurka da a halin yanzu ta cije gam, kamar yadda Go Myong-hyun, mai sharhi a cibiyar Asan mai bincike kan lamurran siyasar duniya ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.