Isa ga babban shafi

Netanyahu ya kare dokar maida Isra'ila ta Yahudawa zalla

Fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya kare dokar da gwamnatinsa ta kafa da ta mayar da kasar ta Yahudawa mabiya addinin Yahudanci zalla.

Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Yayin jawabin da ya gabatar a yau Lahadi, a lokacin da yake taro da ministocinsa, Netanyahu ya ce dokar za ta taimaka, wajen haramtawa Falasdinawa da wasu bakin-haure da suke zaune ba bisa ka’ida ba, neman izinin zama ‘yan kasa.

A makon da ya gabata ne dai gwamnatin Netanyahu ta mika kudirin dokar ga majalisar kasar, wadda bata bata lokaci ba wajen amincewa da ita.

Larabawa mabiya addinin Druze akalla dubu 150,000 ne ke zanga-zangar adawa da dokar ta Isra’ila.

Masu sukar dokar dai na kallonta a matsayin wata kafa ta nuna wariya ga wadanda ba mabiya yahudanci ba, ciki har da Falasdinawa sama da miliyan guda da rabi da ke da shaidar zama ‘yan kasa da kuma wasu mabiya addinan da basu da yawa, ciki har da ‘yan Druze da ke shirin soma zanga-zanga.

Larabawan mabiya addinin na Druze ke da kashi 8 na yawan al’ummar Isra’ila, wadanda suka samu matsayi na musamman a kasar tun a shekarar 1950, a lokacin da aka basu damar shiga cikin rundunar sojin Isra’ila sabanin al’ummar Musulmi da Kiristoci da ke zaune a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.