Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 20/06 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/06 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/06 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 20/06 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/06 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 20/06 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/06 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 20/06 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/06 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/06 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/06 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 20/06 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/06 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/06 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 20/06 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 16/06 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 20/06 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 16/06 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 20/06 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Asiya

Korea ta Arewa ba ta daina kera muggan makamai ba - MDD

media Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, yayin gaisawa da Fira Ministan kasar Korea ta Arewa, Ri Yong Ho yayin taro a kasar, Singapore. 4 ga watan Agusta, 2018. REUTERS/Edgar Su

Wani rahoton majalisar dinkin duniya da ya bayyana ga maneman labarai, ya ce Korea ta Arewa bata dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya da manyan makamai masu linzami ba.

Rahoton wanda wata tawagar kwararru ta majalisar dinkin duniyar ta shafe watanni 6 tana tattarawa, ya kara da cewa, Korea ta Arewan ta na ci gaba da karya takunkuman da kwamitin tsaro na Majalisar ya kakaba mata musamman ta fannin cinikin makamai da man fetur.

A cewar rahoton Korea ta Arewa tana aiki da gwamnatin Syria, domin taimaka mata ta fuskar soji, zalika tana kuma saida makamai ga mayakan ‘yan tawayen Houthi da ke kasar Yemen.

A gefe guda, rahoton ya kuma bankado cewa a tsakanin watan Oktoba na 2017 zuwa Maris na 2018 da muke ciki, Korea ta Arewa ta yi fasa kaurin saida kayayyakin da suka shafi na sawa da darajarsu ta haura dala miliyan 100 a kasashen, China, Ghana, India, Mexico, Sri Lanka, Thailand, Turkiya da kuma Uruguay.

Rahoton ya zo ne a dai dai lokacin da kasashen Rasha da China ke fafutukar ganin, kwamitin sulhu ko na tsaron majalisar dinkin duniya, ya tattauna kan batun sassauta takunkuman karya tattalin arzikin da Amurka ta jagoranci kakabawa Korea ta Arewa, a dalilin shirinta na kera makaman nukiliya da kuma manyan makamai masu linzami.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure