Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta yi watsi da barazanar Amurka ta kakaba mata takunkumi

Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya yi watsi da barazanar takwaransa na Amurka Donald Trump ta kakkabawa kasarsa takunkumi, muddin ta ki sakin wani Fasto Ba Amurke da ta ke tsare da shi.

Shugaban Amurka Donald Trump tare da takwaransa na Turkiya Tayyip Erdogan, yayin tattaunawa a taron kungiyar NATO da ya gudana a babban birnin Belgium, Brussels. 11 ga watan Yuli, 2018.
Shugaban Amurka Donald Trump tare da takwaransa na Turkiya Tayyip Erdogan, yayin tattaunawa a taron kungiyar NATO da ya gudana a babban birnin Belgium, Brussels. 11 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Kevin Lamarque/File Photo
Talla

A halin yanzu jami’an tsaron Turkiya sun mayar da Fasto Andrew Brunson zuwa daurin talala a gida, bayan shafe watanni 21 tsare a wani kurkukun kasar.

Fasto Brunson wanda ya shafe sama da shekaru 20 yana aiki a Turkiya, ya fada komar jami’an tsaronta ne, bayan da gwamnatin Erdogan ta zarge shi da bayar da gudunmawa a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, cikin shekarar 2016.

Gwamnatin Turkiya ta na kuma zargin Fasto Brunson da goyon bayan haramtaciyyar jam’iyyar neman ‘yancin Kurdawa ta PKK, wadda shugabancin kasar ta Turkiya ya bayyana tabbacin tana da hannu a yukunrin juyin mulkin.

Muddin wannan zargi da Faston ke musantawa ya tabbata akansa, to fa za’a zartas masa da hukuncin daurin shekaru akalla 35.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.