Isa ga babban shafi
Yemen

'Yan tawaye sun zargi kawancen Larabawa da karya yarjejeniyar 'Hodeida

Yan tawayen Yemen sun zargi dakarun kwancen kasashen larabawa karkashin jagorancin kasar Saudiya da kai hare hare a yankunan birnin nan mai tashar jiragen ruwa na 'Hodeïda.

jagoran yan tawayen Huti a kasar Yemen
jagoran yan tawayen Huti a kasar Yemen AL-MANAR TV / AFP
Talla

wannan zargi dai ya biyo bayan wani ikrari ne da yan tawayen suka yi awowi 24 da suka gabata inda suka ce, sun  yi barin wuta kan filin sauka da tashin jiragen saman Abu Dhabi na kasar daular larabawa.

Sai dai ko a bangaren  mahukumtan na daular larabawa da na kasar Saudiya, babu wanda ya fito ya  tabbatar ikrarin na yan tawaye

idan dai ba a manta ba a ranar 1 ga watan yunin da ya gabata ne, a karkashin shiga tsakanin Majalisar Dinkin Duniya  aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin na Hodeda,  tsakanin dakarun dake goyon bayan gwamnatin yamen dake samun tallafin kasashen larabawa da Saudiya ke jagoranta,  da kuma  yan tawayen Hutidake samun goyon bayan kasar Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.