Isa ga babban shafi
Afghanistan-Ta'addanci

Harin bam ya hallaka mutum 11 a gab da filin jirgin saman Kabul

Wani Dan kunar bakin wake ya tada bam kusa da hanyar shiga tashar jiragen saman birnin Kabul da ke kasar Afghanistan inda ya kashe akalla  mutane 11, ya kuma raunana wasu 14.

Hare-hare sun ci gaba da tsananta a sassan kasar ta Afghanistan ne tun bayan kawo karshen tsagaita wuta tsakanin gwamnati da Taliban.
Hare-hare sun ci gaba da tsananta a sassan kasar ta Afghanistan ne tun bayan kawo karshen tsagaita wuta tsakanin gwamnati da Taliban. REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Rahotanni sun ce an kai harin ne kan gangamin jama’ar da suka je tashar jiragen domin tarbar mataimakin shugaban kasar Abdul Rashid Dostum wanda ke komawa bayan gudun hijira.

Kakakin mataimakin shugaban, Bashir Ahmad Tayanj, ya ce babu abinda ya samu mai gidan nasa wanda ke cikin motar yaki ta soji.

Tuni jami'an agaji suka kwashe mutanen da suka jikkata don ba su kulawar gaggawa a asibiti.

Hare-hare dai sun kara tsananta a sassan kasar ta Afghanistan tun bayan kawo karshen tsagaita wutar da aka yi tsakanin gwamnati da Kungiyar Taliban, duk kuwa da kiraye-kirayen da ake ci gaba da yi don sasantawa tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.