Isa ga babban shafi

Turkiya za ta dage dokar ta bacin da ta kafa a makon gobe

Gwamnatin Turkiya ta ce a mako mai kamawa za ta dage dokar ta bacin da ta kafa a ilahirin kasar, tun a shekarar 2016, bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan. REUTERS/Umit Bektas
Talla

Ibrahim Kalin, wanda shi ne Kakakin shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan ya shaidawa manema labarai a birnin Ankara cewar a ranar 18 ga watan Yulin na shekarar 2018 da muke ciki, za a kawo karshen aikin dokar ta bacin.

A karkashin dokar ta bacin dai, shugaba Erdogan ya kori ma’aikatan gwamati sama da dubu 110, tare da dakatar da wasu dubban, sakamakon zargin suna da alaka da malamin addinin Fetullah Gulen da aka zarga da kitsa yunkurin juyin mulkin.

Sai dai Gulen wanda ke gudun hijira a Amurka na ci gaba da musanta zargin da ke masa.

Sanarwar dai ta zo ne, bayan da shugaba Erdogan ya jagoranci taron ministoci da sauran mukarraban gwamanatinsa karo na farko, bayan samun nasara a zaben shugabancin kasar, a matsayin shugaba mai cikakken iko da ya kara samun karfin zartas da dokoki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.