Isa ga babban shafi

Tsugunno bata kare ba tsakanin Korea ta Arewa da Amurka

Gwamnatin Korea ta Arewa ta yi watsi da ikirarin sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, wanda ya ce ganawar da ya yi da wakilan kasar, yayin ziyarar kwana guda da yini da ya kammala a ranar Asabar 7 ga watan Yuli 2018, ta samu ci gaba dangane da shirin lalata makaman nukiliyarta na din din din.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yayin bankwana da Kim Yong Chol, babban jami'in jam'iyya mai mulkin Korea ta Arewa, a filin jiragen sama na Sunan da ke birnin Pyongyang.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yayin bankwana da Kim Yong Chol, babban jami'in jam'iyya mai mulkin Korea ta Arewa, a filin jiragen sama na Sunan da ke birnin Pyongyang. AFP
Talla

Sai dai jim kadan bayan tashin sakataren wajen na Amurka zuwa Japan korea ta Arewa ta yi watsi da ikirarin nasa tare da bayyana bukatun Amurkan kan nukiliyarta a matsayin na son zuciya da hadama.

A watan Yuni da ya gabata, bayan tattaunawa da takwaransa na Amurka a kasar Singapore, shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-un ya amince da kawo karshen shirin mallakar makaman nukiliyar da gwamnatinsa ta yi nisa a kai.

A karkashin yarjejeniyar da aka cimma a tattaunawar ta ranar 12 ga watan Yuni 2018, idan Korea ta Arewan ta cika alkawari, Amurkan za ta kawo karshe atasyen sojin hadin gwiwa da ta ke yi da Korea ta Kudu, tare da dage tarin takunkuman karya tattalin arzikin da aka kakabawa Korea ta Arewan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.