Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Shugaba Ashraf na Afghanistan ya yi umarnin kai farmaki kan Taliban

Jami’an tsaron kasar Afghanistan sun koma bakin aikin kai farmaki kan mayakan Taliban bayan da shugaba Ashraf Ghani ya tabbatar da kwao karshen yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin gwamnatin kasar da mayakan.

Shugaba Ashraf Ghani ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar ta nuna yadda galibin mayakan na Taliban suka kosa da yakin da su ke da Gwamnati.
Shugaba Ashraf Ghani ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar ta nuna yadda galibin mayakan na Taliban suka kosa da yakin da su ke da Gwamnati. DR
Talla

A bayanan da ya gabatar shugaba Ashraf, ya ce bayan kara akalla kwanaki 18 kan wa’adin da aka dauka tun da farko na tsagaita wutar kwanaki don gudanar da bukukuwan sallah lafiya.

A cewarsa yarjejeniyar ta tafi yadda ya kamata da akalla kasha 98, sai dai hakan ba zai hana ci gaba da kai farmaki kan mayakan na Taliban ba kowanne lokaci daga yau Asabar.

Kusan dai ilahirin bangarorin biyu sun gamsu da yarjejeniyar tsagaita wutar ta yadda kowanne bangare ya gudanar da bukukuwan sallah cikin lumana.

An dai ga mayakan na Taliban, karon farko cikin shekaru 17 da suka shafe suna yaki da gwamnatin kasar na gudanar da bikin sallah a wannan karon cikin farin ciki, inda suka rika musafaha da juna tare da daukar hotuna da ‘yan uwansu.

Shugaba Ashraf Ghani ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar ta nuna yadda galibin mayakan na Taliban suka kosa da yakin da su ke da Gwamnati.

A cewarsa galibin mayakan na fatan ajje makamansu tare da rungumar zaman lafiya amma shugabancin kungiyar ba zai bar sub a.

Shugaban na Afghanistan Ashraf Ghani ya ce yanzu zabi ya rage ga kungiyar kan ta amince da tattaunawar sulhu da kawo karshen yakinta ko kuma ta zabi ci gaba da yakin a dai dai lokacin da dakarun kasar za su koma kai mata farmaki daga gobe Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.