Isa ga babban shafi
Indonesia

Ana ci gaba da neman mutane a hadarin jirgin ruwa a Indonesia

Yanzu haka ana cigaba da neman mutane 192 da suka bata bayan da wani jirgin ruwa da suke ciki ya kife tun ranar litinin a tsibirin Toba da ke kasar Indonesia.Shugaban hukumar agajin gaggawa da ke gudanar da aikin bincike dangane da faruwar hatsarin, ya ce babu cikakkun alkaluma dangane da adadin mutanen da cikin kwale-kwalen kafin kifewarsa.

Jirgin ruwa da ya kife tun ranar litinin a tsibirin Toba na kasar Indonesia
Jirgin ruwa da ya kife tun ranar litinin a tsibirin Toba na kasar Indonesia IVAN DAMANIK / AFP
Talla

Kwale-kwalen ya tashi ne daga tsibirin Toba zuwa Sumatra dauke da mutanen da aka tabbatar da cewa adadinsu ya haura 200, kuma ga alama jirgin ba ya da izinin gudanar da jigilar fasinja a wannan tsibiri.

Shaidu sun ce a lokacin da ya tashi daga tashar ruwan Toba, ko baya ga dimbin mutane, har ila yau akwai kayayyaki ciki har da babura akalla 80 a cikinsa, duk da cewa an kera shi ne domin daukar mutanen da adadinsu bai wuce 43 ba.

Daga lokacin kifewarsa zuwa yau, duka duka gawarwakin mutane 4 kawai ne aka gano, yayin da aka gano wasu mutane 18 da rayukansu.

To sai dai a cewar Muhammad Syaugi shugaban aikin ceton, bayan tattara shaidu daga iyalan fasinjojin wannan karamin jirgin, an fahinci cewa adadin mutanen da har yanzu ba a kai ganowa ba zai kai 192.

Jami’ai sama da 400 ne aka tura zuwa yankin domin gudanar da aikin ceton.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.