Isa ga babban shafi

Amurka da Korea ta Kudu sun dakatar da atasayen soji

Kasar Amurka da Korea ta Kudu, sun sanar da dakatar da atasayen soji na hadin gwiwa da suke yi a yankin Korea.

Wasu sojin Korea ta Kudu yayin atasayen hadin gwiwa da sojin Amurka a Kudu maso gabashin tashar ruwan garin Pohang a shekarar 2017.
Wasu sojin Korea ta Kudu yayin atasayen hadin gwiwa da sojin Amurka a Kudu maso gabashin tashar ruwan garin Pohang a shekarar 2017. AFP/File / JUNG Yeon-Je
Talla

Matakin ya zo ne mako guda, bayan da Shugaba Trump yayi alkawarin dakatar da atasayen bayan kammala ganawa da takwaranshi na Korea ta Arewa Kim Jong Un a kasar Singapore.

Korea ta Kudu ta sanar da cewa matakin zai shafi wani babban atasayen wanda a baya aka shirya zai gudana a watan Agusta mai zuwa, wanda ake sa ran sojin Amurka akalla 17,500 zasu halarta, to amma har yanzu ba’a kai ga tantance ko shi ma katafaren atasayen za a fasa gudanar da shi ba.

Sai dai kasashen zasu maido da shirin asatasyen sojin muddin Korea ta Arewa ta gaza cika alkawarinta na yin watsi na din din din da shirinta na mallakar makaman nukiliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.