Masu tattaki a Afghanistan don samar da zaman lafiya sun isa Kabul
Masu fafutukar samar da zaman lafiya a kasar Afghanistan wadanda suka yi tattaki na tsawon kilomita 700 a cikin kwanaki 40, a yau litinin sun isa Kabul fadar gwamnatin kasar.
Wallafawa ranar:
Masu tattakin sun zagaya a biranen kasar da dama a kafa a duk tsawon watan Ramadana, inda suke yi kira ga gwmanatin da kuma ‘yan Taliban da su rungumi zaman lafiya.
Sai dai kuma Isar masu faftukar birnin Kabul na zuwa a dai dai lokacin da Taliban ta yi watsi da tayin kara wa'adin tsagaita wuta tsakaninsu da Sojin kasar da kuma na hadaka.
Tun farko dai gwamnatin ce ta bukaci tsagaita wutar don gudanar da bukukuwan sallah Lafiya inda kuma daga bisani ta bukaci tsawaita wa'adin amma Taliban ta ki.
Fatan masu faftukar bai wuce ganin an kawo karshen rikicin da ke tsakanin bangarorin biyu ba, tare da ganin an samu wanzuwar zaman lafiya a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu