Nicaragua
Kokarin shawo kan Shugaba Ortega ya citura
Shugabanin darikar Katolika a Nicaragua sun gana da shugaban kasa Daniel Ortega domin ganin sun shawo kan sa dan farfado da tattaunawar da zata kawo karshen rikicin siyasar kasar wanda tuni ta kai ga hallaka mutane 134, sai dai rahotanni sun ce babu abinda da taron ya cimma.
Wallafawa ranar:
Talla
Shugaban mabiya darikar dake Managua, Silvio Jose Baez yace shugaba Ortega ya bukace su da su bashi lokaci domin nazari kan bukatun da suka gabatar masa.
Yan adawa sun bukaci ganin shugaban ya amince da wani sabon shirin tattaunawa domin tabbatar da dimokiradiya a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu