China
Mota dauke da nakiyoyi ta tarwatse a gaf da ramin hakar ma'adanai a China
A kasar China, wata mota dauke da nakiyoyi ta tarwatse dab da wani ramin hakar ma’adinai a wani yankin arewa maso gabashin kasar, kuma mutane akalla 11 suka mutu nan take wasu 25 kuma na chan sun makale cikin rami.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Ma’aikatan hakar ma’adinan na aikin su ne a lokacin da aka sami tsautsayin.
Jami’an ma’aikatar kai daukin gaggawa na kasar da kuma jamian yankin Benxi inda aka sami tsautsayin na ci gaba da aikin ceto.
Kasar China na daga cikin kasashe da ake yawan samun hadura a wurraren hakar arzikin ma’adinan karkashin kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu