Isa ga babban shafi

China za ta soke dokar kayyade haihuwa

Gwamnatin China ta fara nazari kan daukar matakin soke dokar kayyade yawan yaran da ma’aurata zasu Haifa, wadda ta kafa a shekarun baya.

A shekarar 2015 kididdiga ta nuna cewa yawan al'ummar China ya kai biliyan 1.375.
A shekarar 2015 kididdiga ta nuna cewa yawan al'ummar China ya kai biliyan 1.375. Reuters
Talla

Wannan shawara ta biyo bayan binciken baya bayan nan da ya nuna cewa yawan al’ummar kasar ta China yana raguwa kashi 3.5, wato kwatankwacin mutane miliyan 17, duk kuwa da matakin da gwamnati ta dauka a shekarar 2015 na baiwa ma’aurata dama kara haihuwar yara biyu a maimakon daya.

Wani lokaci a karshen wannan shekara ko cikin mai kamawa ta 2019 ake sa ran China zata zartas da soke dokar kayyade haihuwar.

A shekarar 1970 China ta kafawa ma’aurata dokar kayyade haihuwar yaro guda kawai, sai dai sakamakon wani bincike da masana suka gudanar ya nuna cewa dokar ta haifar da matsalar rashin daidaito tsakanin yawan maza da mata a kasar.

Rahoton binciken ya ce zuwa karshen shekara ta 2017, yawan maza ya zarta na mata a kasar ta China da akalla miliyan 32.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.