Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta yi barazanar janye tattaunawa da Amurka

Shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-Un ya yi barazanar janye batun tattaunawar sulhu da Shugaban Amurka Donald Trump matukar kasar ta bukaci lallai sai ta lalata makamanta na Nukiliya.

Sanarwar da Amurka ta fitar a baya-bayan nan ta ce a shirye ta ke ta ga tattaunawar sulhun ta gudana, amma kuma matukar Korea ta arewan ta toge to babu shakka za su ci gaba da kakaba mata takunkumai.
Sanarwar da Amurka ta fitar a baya-bayan nan ta ce a shirye ta ke ta ga tattaunawar sulhun ta gudana, amma kuma matukar Korea ta arewan ta toge to babu shakka za su ci gaba da kakaba mata takunkumai. Mandel Ngan / AFP / KCNA VIA KNS
Talla

Barazanar ta Kim na zuwa ne a dai dai lokacin da ya rage kwanaki kalilan a yi wata tattaunawar kai tsaye tsakanin Kim din da Donald Trump wadda ake saran ta kawo karshen takun sakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Sai dai kuma a wata sanarwa cikin fushi da mataimakin ministan da ke kula da harkokin kasashen waje na Korea ta Arewan Kim Kye-gwan ya fitar, ta zargi Amurka da boye wani kulli tare da mummunar manufa kan shirin na su na tattaunawar sulhun wadda za ta gudana ranar 12 ga watan Yuni.

Sanarwar ta Mr Kye-gwan ta ce Korea ta Arewan sam ba za gamsu da babban mashawarcin Trump kan harkokin tsaro John Bolton ba, kuma ba za ta iya boye rashin gamsuwar da ta yi da shi ba.

Sai dai kuma wata sanarwar baya-bayan nan da Fadar White House ta Amurka ta fitar, ta ce har yanzu tana fatan tattaunawar sulhun ta gudana.

A cewar mai magana da yawun fadar ta Amurka Sarah Sanders, Trump a shirye ya ke tattaunawar ta gudana lafiya, amma matukar Korea ta arewan ta toge, babu shakka za su ci gaba da dora manyan takunkumai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.