Isa ga babban shafi
Iran

Iran ta musanta tallafawa 'yan awaren Polisario da makamai

Iran ta musanta hannunta a tallafawa 'yan awaren Polisario masu fafutukar kafa kasa mai cin gashin kanta a yammacin Sahara, ta hanyar aike musu da tarin makamai. Kalaman na Iran na zuwa ne kwana guda bayan Morocco ta sanar da yanke huldar diflomasiyya da ita kan zargin.

Iran ta ce duk da Moroccon ba ta da wata hujja kan zargin da ta ke mata amma ita ma ta amsa katse alakar.
Iran ta ce duk da Moroccon ba ta da wata hujja kan zargin da ta ke mata amma ita ma ta amsa katse alakar. ADEM ALTAN / AFP
Talla

Morocco wadda ta yanke duk wata huldar jakadanci da Iran din wadda ke matsayin babbar abokiyar gabar Saudiyya, ta yi zargin cewa Iran din na amfani da sojin kawancenta na Hizbullah da ke Lebanon wajen mikawa 'yan tawayen na Polisario da tarin makamai.

Ko da ya ke dai Iran din ta musanta batun tare da zargin cewa Moroccon ta fake da 'yan tawayen na Polisario ne don yanke huldar da ke tsakaninsu wadda dama ta jima tana neman hanyar yin hakan.

Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Iran din ta fitar a yau, ta ce babu gaskiya cikin zarge-zargen kuma ita tana yin dukkan mai yiwuwa wajen mutunta dokokin tsaron kasa da kasa.

Sanarwar ta ce duk da Moroccon ba ta da wata hujja kan zargin da ta ke mata amma ita ma ta amsa katse alakar.

Tuni dai Saudiyya ta yi marhabin da matakin na Morocco wanda ta ce zai kawo karshen tsoma bakin da Iran din ke yi a harkokin cikin gidan Morocco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.