Isa ga babban shafi
Iran

Babu alamun Iran na da shirin kera makamin nukiliya- IAEA

Hukumar hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, ta ce har yanzu ba wasu gamsassun hujjoji da ke tabbatar da cewa Iran na da wani shiri domin kera makaman nukiliya.Hukumar ta IAEA na mayar da martani ne a game da sanarwar da firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu ya fitar a marecen jiya, inda ya ke zargin Iran da boyewa duniya gaskiya dangane da shirinta na nukiliya.

Tawagar hukumar hana yaduwar makaman nukiliya a duniya IAEA.
Tawagar hukumar hana yaduwar makaman nukiliya a duniya IAEA. KAZEM GHANE / IRNA / AFP
Talla

Sanarwar da hukumar ta IAEA wadda ke karkashin MDD ta fitar, ta ce daga 2009 zuwa yau, ba wata hujjar da ke tabbatar da cewa Iran na da wani boyayyen shiri da ya shafi nukiliya, kuma rahoton da Kwamitin Koli na Hukumar ya gabatar a shekara ta 2015 tuni ya wanke kasar daga wannan zargi.

Wannan dai na a matsayin mayar da martani ne ga ga Firaminista Benyamin Netanyahu, wanda a marecen jiya ya bayyana wa duniya cewa yana da cikakkun hujjoji Iran za ta iya farfado da wannan shiri na nukiliya a duk lokacin da ta ga dama.

Uwargida Federica Moghereni, shugabar ofishin kare manufofin ketate ta Tarayyar Turai, Kungiyar da ta taka gagarumar rawa domin kulla yarjejeniyar 2015 wadda ta kawo karshen shirin nukiliyar Iran hatta wanda ba ya da alaka da aikin soji, ta ce a iya saninsu dai Iran na cigaba da mutunta sharuddan da aka gindaya ma ta.

Sanarwar da ma’aikatar wajen Iran ta fitar jim kadan bayan zargin na Firaministan Isra’ila kuwa, ta bayyana Netanyahu a matsayin makaryaci, wanda kuma ba ya da wata kwarewa face zubar da jinin jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.