Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

'Yan Korea ta kudu na dari-dari kan tattaunawar kasar da Korea ta Arewa

A dai dai lokacin da kasashen Korea ta kudu da makwabciyarta Korea ta arewa ke gab da tattaunawa a gobe Juma'a, har yanzu wasu daga cikin al'ummar Korea ta kudun na ci gaba da zaman dar-dar kan yiwuwar dorewar zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.

Har yanzu dai wasu al'ummar Korea ta kudu na ganin babu gaskiya a batun dakatar da shirin nukiliyar Korea ta arewa.
Har yanzu dai wasu al'ummar Korea ta kudu na ganin babu gaskiya a batun dakatar da shirin nukiliyar Korea ta arewa. REUTERS
Talla

A yau Alhamis ne dai shugabannin kasashen biyu Moon Jae-in da Kim Jong Un za su gana a dai dai layin da ke kan iyakar kasashen biyu gabanin fara tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu a gobe Juma'a.

Matukar dai Kim ya tsallaka layin babu shakka zai zamo shugaban Korea ta arewa na farko da ya tsoma kafar shi a Korea ta kudu tun bayan yakin basasar kasashen shekaru 65 da suka gabata.

Haka zalika ganawar shugabannin biyu za ta zamo ita ce irinta ta 3 da aka taba gudanarwa tsakanin shugabannin kasashen biyu da ta kunshi ta shekarar 2000 da ta 2007.

Sai dai kuma yayinda bangarorin biyu ke ci gaba da shirye-shiryen tattaunawar tare da kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu tsawon shekaru wasu al'ummar Korea ta kudu na ganin har yanzu akwai bukatar darri-dari da Korea ta arewan.

Wani farfesa da ya fito daga Korea ta kudun Lew Je-bong wanda yana yaro aka yi yakin basasar kasashen, ya ce dole ne Koreaa ta kudu ta yi taka-tsan-tsan la'akari da yadda takwararta ta ta kware wajen makirci da karya.

A cewarsa karya alkawari ba sabon al'amari ba ne ga Korea ta arewa tarihi ya nuna hakan, yana mai cewa fatansu bai wuce kada Korea ta arewan ta yi amfani da su bane kawai domin babu yadda za a yi ta iya dakatar da shirinta na Nukiliya.

Sai dai kuma a bangaren Lee Jeong-jin wani fitaccen dan kasuwa a Korea ta kudun ya ce sai da ya zubar da hawaye lokacin da ya ji batun tattaunawar kasashen biyu, yana mai cewa yanzu zaman lafiya zai dawo tsakanin 'yan uwan juna.

Kawo yanzu dai shugaban Amurka Donald Trump bai furta tsayayyiyar ranar da zai tattauna da Kim ba, sai dai ya ce zai zabu da ya daga cikin karshen watan Mayu ko kuma farkon Yuni don ganawa da takwaran na sa na Korea ta Arewa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.