Isa ga babban shafi
Amurka-korea ta Arewa

Amurka ta fara tattaunawar kai tsaye da Korea ta Arewa

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewar sun fara tuntibar juna kai tsaye tsakanin jami’an Amurka da na Koriya ta Arewa domin kawo karshen tankiyar dake tsakanin kasashen biyu.

Kim Jong-un, Shugaban Korea ta Arewa
Kim Jong-un, Shugaban Korea ta Arewa KCNA/via Reuters
Talla

Yayin ganawa da Firaministan Japan, Shinzo Abe a Florida, shugaba Trump yace akwai fatar gudanar da taro tsakanin kasashen biyu cikin kwanaki 10 masu zuwa, domin kawo karshen rashin jituwar da ta kaiga yakin Koriya tsakanin shekarar 1950 zuwa 1953.

Rahotanni sun ce shugaban hukumar CIA Mike Pompeo wanda Trump ya nada a matsayin wanda zai maye gurbin Rex Tillerson a matsayin Sakataren harkokin waje, ya ziyarci Koriyar a asirce a farkon watan nan inda ya gana da shugaba Kim Jong Un.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.