Isa ga babban shafi
Rasha-Syria

Turkiyya da Iran da Rasha sun sha alwashin hana Syria kifewa

Ofishin shugaban kasar Turkiyya ya sanar cewar kasashen Turkiyya da Iran sun lashi Takobin marawa kasar Rasha baya, domin hana wa kasar Syria kifewa. Wannan na faruwa ne bayan goyon bayan da kasar Turkiya ta bai wa kasar Amurka domin kai wa shugaba Assad na Syria hari.

Shugaba Erdogan na Turkiya Putin na Rasha da Rohani na Iran
Shugaba Erdogan na Turkiya Putin na Rasha da Rohani na Iran AFP
Talla

Shugabannin kasashen Turkiyya da Iran duka sun hada kai domin goyon bayan Rasha akan batun hanawa kasashen yammacin Duniya kifar da Gwamnatin ta Assad da tuni Amurka ta fara kai wa farmaki.

Wata majiya kwakkwara da ta jiyo daga hirar da shugabannin biyu wato Recep Teyep Erdogan na Turkiyya, da Hassan Rouhani na kasar Iran suka yi a wayar Tarho ce ta tabbatar da cewar kasashen dai sun bayyana aniyarsu ta tabbatar da ganin an warware matsalar ta fadan da ake a Syria cikin ruwan sanyi.

Wannan hadin kai na kasashen guda uku dai na dai daga cikin abubuwan da suka hana wa Turawan yammacin Duniya sauya Gwamnati a Syria, musamman lura da yadda yakin da Gwamnatin Assad ke yi da 'yan tawayen ya share sama da shekaru 7.

Ko baya ga kai harin da aka yi a karshen makon da ya gabata a Syria, Dakarun gwamnatin Assad sun bayyana nasarar kama a birnin Sanaa dai daga cikin biranen da 'yan tawayen sua yi kaka-gida baya ga birnin Douma da ke makwabtaka da birnin Damascus.

Syria dai kasa ce mai arzikin albarkatun kasa, kuma shugaba Bashar al-Assad ya gaji mulkin kasar ne daga mahaifinsa, wanda a wannan lokacin yana dasawa da kasar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.