Isa ga babban shafi
Myanmar

Iyalan farko na yan gudun hijira Rohingya sun koma gida

Gwamnatin kasar Myanmar ta bayyana maido da Iyalan na farko daga cikin ‘yan gudun hijirar Rohingya dubu 700 da suka gudu suka bar kasar a lokacin da Sojin kasar ke fatattakarsu daga matsugunnansu.

Yan gudun hijirar Rohingya
Yan gudun hijirar Rohingya REUTERS/Andrew RC Marshall
Talla

Gamnatin kasar dai ta sanar da hakan ne a wani mataki na nunawa Duniya cewar an fara samun jituwa tsakaninsu da ‘yan gudun hijirar na Rohigya.

To sai dai har yanzu abinda ake shakku shi ne makomar tsaron mutanen da suka fara komawa a gidajensu, musamman lura da yadda suke fuskantar kyama daga al’ummar kasar.

Yan gudun hijirra Rohingya musulmin dai sun yi yawa a wani sansanin ‘yan gudun hijira da ke a kasar Bangladesh, tun lokacin da Sojin kasar suka fara kai masu hare-hare a yankin arewacin jihar Rakhine a watan Agustan da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.