Isa ga babban shafi
Syria

Sojin Syria sun kwace kashi 90 na gabashin Ghouta

Bayan kwashe sama da wata guda jiragen yakin Syria na luguden wuta akan yankin Gabashin Ghouta, mayakan ‘yan tawayen kasar sun amince da ficewa daga yankunan da ke karkasinsu a baya, illa birnin Douma da ke yankin.

Wasu daga cikin mayakan 'yan tawayen Syria da suka janye daga gabashin Ghouta, tare da Iyalansu.
Wasu daga cikin mayakan 'yan tawayen Syria da suka janye daga gabashin Ghouta, tare da Iyalansu. REUTERS/ Omar Sanadiki
Talla

A halin yansu kashi 90 na yankin gabashin Ghouta na karkashin ikon sojin Syria, tun bayan da suka kaddamar da farmaki kan ‘yan tawaye a ranar 18 ga watan Fabarairu, wanda masu sa ido suka ce akalla mutane 1,600 suka hallaka sakamakonsa.

Wannan ce dai nasara mafi girma da gwamnatin Shugaban Syria Bashar al-Assad ya samu bayan fatattakar ‘yan tawayen da yayi daga birnin Aleppo a watan Disambar shekara ta 2016.

Majalisar dinkin duniya ta yi hasashen cewa akalla mutane 400,000 farmakin jiragen yakin Syrian kan ‘yan tawaye a Ghouta ya rutsa da su, wadanda basa samun abinci da magunguna.

Akalla mutane 7000 ne suka amince da barin garuruwan Arbin, Joba, Zamlka da Ein Terma, ciki harda mayakan ‘yan tawaye da kuma iyalansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.