Isa ga babban shafi
Afghanistan

Harin bam ya kashe mutane 10 a Afghanistan

Akalla mutane 10 sun rasa rayukansu bayan wata mota makare da bama-bamai ta tarwatse a kusa da wani filin wasa da ke kudancin Afghanistan mai fama da rikici.

Dan kunar bakin wake ya yi amfani da motarsa makare da bama-bamai wajen kai farmaki a Afghanistan
Dan kunar bakin wake ya yi amfani da motarsa makare da bama-bamai wajen kai farmaki a Afghanistan REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Harin ya auku ne a a birnin Lashkar Gah a dai dai lokacin da ma’abota kallon wasanni ke ficewa daga filin wasan, bayan kammala wata gasar dambe.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Lardin Helmand, Salam Afghan, ya tabbatar da mutuwar mutane 10 tare da jikkatar wasu 35 da suka hada da kananan yara.

Maharin ya tayar da bama-baman da ke cikin motarsa ne bayan jami’an tsaro sun gano shi a dai dai lokacin da yake kokarin kutsawa cikin filin wasan.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da farmakin na yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.