Isa ga babban shafi
Afghanistan

Taliban ta dau nauyi wani harin kunar bakin wake da ya hallaka mutane biyu a Kabul.

Wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota da kuma kungiuyar Taliban ta dau nauyi kaiwa a yau assabar a Kabul babban birinin kasar Afghanistan ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane biyu a yayinda wasu da dama suka jikkata kamar yadda ofishin ma’aikatar cikin gidan kasar ta sanar.

motocin da suka kone a wani harin kunar bakin wake da Taliban ta kai a Jalalabad, Afghanistan 24,ga watan janairu 2018.
motocin da suka kone a wani harin kunar bakin wake da Taliban ta kai a Jalalabad, Afghanistan 24,ga watan janairu 2018. REUTERS/Parwiz
Talla

Kakakin ma’aikatar ministan cikin gidan Najib Danish, ya sanar da Afp cewa harin ya wakana ne da misalign karfe 9:10 na safe a gogon kasar kuma kawo yanzu mutane biyu fararen hula ne aka tabbatar da mutuwarsu a yayinda wasu 4 su ka jikkata kamar yadda kakakin ofishin ma’aikatar kiyon lafiyar kasar Wahid Majrooh ya sanar

Mataimakin ministan cikin gidan Afghanistan, Nasrat Rahimi, ya bayyana cewa dan kunar bakin waken ya yi niyar kai harin ne a kan wani kamfanin tsaro na kasar britaniya, G4S, ne saidai ya tarwatsa kansa kafin kaiwa ga inda aka nufa.

A cikin wani sako ta WhatsApp, kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya bayyana cewa dan kunar bakin waken ya kai harin ne a kan wani ayarin motocin tawagar baki yan kasashen ketare kuma dukkanin wadanda ke cikin a motar sun mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.