Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 22/03 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/03 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/03 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 22/03 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/03 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 22/03 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/03 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 22/03 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/03 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/03 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/03 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 21/03 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/03 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/03 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 21/03 16h40 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 17/03 20h00 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 21/03 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 17/03 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 21/03 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Asiya

Myanmar za ta mayar da 'yan kabilar Rohingya muhallansu

media Kungiyoyin kare hakkin dan adama na duniya dai na ci gaba da jan hankalin gwamnatin ta Myanmar kan kiyayen rayukan 'yan kabilar ta Rohingya da ke a matsayin tsirarun musulmi a kasar ta mabiya addinin Budda. REUTERS/Andrew RC Marshall

Gwamnatin Myanmar ta ce ‘yan gudun hijirar musulmi ‘yan kabilar Rohingya ke shirin komawa jihar Rakhine ba za su dawwama a sansanin ‘yan gudun hijira ba, face sai ta tabbatar da kowannensu ya koma muhallinsa na asali.

Mynamar dai ta samar da guraben da za ta sauki daruruwan ‘yan kabilar ta Rohingya da ke gudun hijira a Bangladesh amma kawo yanzu babu ko da mutum guda cikin fiye da mutane dubu dari 7 da ya koma jihar tun bayan kisan kiyashin da jami’an tsaron kasar suka rika yi musu bayan wani rikici tsakaninsu da mabiya addinin Budda a kasar mai karancin musulmi.

Majalisar dinkin Duniya ta ce matukar da gaske Mynamar din na bukatar komawar daruruwan ‘yan kabilar ta Rohingya dole ne ta dauki matakan kare rayukansu.

A bangare guda suma daruruwan ‘yan gudun hijirar da ke zaune a bangaladesh karkashin wata kungiya guda da suka kafa sun bukaci lallai Myanmar ta cika musu wasu sharudda da suka gindaya kafin amincewa da komawarsu jihar Rakhine.

Daga cikin sharuddana da suka gindaya akwai sakar musu mutanensu da gwamnatin ke rike da su a gidajen yari, sai kuma batun tabbatar da su a matsayin cikakkun ‘yan kasa baya ga alkawarin kare rayukansu.

Ko a baya dai Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rikicin na Myanmar a matsayin yunkurin shafe wata kabila, matakin da ya sa ta bukaci shugabar gwamnatin ta Myanmar Aung San Suu Kyi yi mata bayani kan matakan da take dauka don kare rayukan 'yan kabilar ta Rihingya amma ta gaza cewa uffan.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure