Isa ga babban shafi
Syria

Yakin Syria ya cika shekaru 7 da barkewa

Yau Alhamis yakin da ake fafatawa a kasar Syria ya cika ke cika shekaru bakwai da barkewa, inda ake ci gaba da fafatawa tsakanin ‘yan tawayen da ke neman kawar da gwamnatin shugaba Bashar Al Assad wanda shi kuma ke cewa yana yaki ne da yan ta’adda.

Wasu fararen hula a Syria yayin da suke gudun ceton rai, sakamakon luguden bama-baman da jiragen yaki ke yi a yankin Gabashin Ghouta, da ke wajen birnin Damascus.
Wasu fararen hula a Syria yayin da suke gudun ceton rai, sakamakon luguden bama-baman da jiragen yaki ke yi a yankin Gabashin Ghouta, da ke wajen birnin Damascus. Abdulmonam Eassa/AFP
Talla

Zuwa yanzu wannan yaki ya lakume rayukan mutane sama da dubu 465, yayin da wasu ‘yan kasar ta Syria sama da miliyan 20 suka zama ‘yan gudun hijira a ciki da wajen kasar.

A ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2011, aka fara zanga-zangar lumana a kasar ta Syria, biyo bayan juyin juya halin da ‘yan kasashen Tunisia da Masar suka yi, wanda ya basu nasarar kawar da shugabanninsu a waccan lokacin.

Sai dai zanga-zangar kin jinin gwamnatin ta Bashar al-Assad a Syria, ta juye zuwa yakin basasa, bayanda ‘yan adawa suka zargi gwamnati da kashe daruruwan masu adawa da ita ba, garkame da dama kurkuku da kuma azabtar da su.

Har yanzu ba’a samu nasarar yukurin dawo da zaman lafiya a kasar ba, duk da cewa Majalisar Dinkin Duniya, da kuma manyan kasashen duniya da suka hada da Rasha, Amurka, Iran, Turkiya, Faransa da kuma Birtaniya suna ci gaba da kokarin ganin an kawo karshen yakin da kuma sulhunta gwamnati da ‘yan adawa.

Daya daga cikin batutuwan da ake ganin sun taka rawa wajen gaza cimma burin shawo kan wannan kazamin yaki shi ne banbacin manufofin diflomasiyya da ke tsakanin bangarorin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.