Isa ga babban shafi

Macron da Modi sun rattaba hannu akan yarjejeniyoyi 50

Akalla yarjejeniyoyi 50 shugaban Faransa Emmanuel Macron da Fira Ministan India Narendra Modi suka sanya wa hannu, bayan ganawarsu ta farko a ziyarar kwanaki hudu da shugaban na Faransa ke yi a kasar ta India.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Fira Ministan India Narendra Modi, a birnin New Delhi a ranar Asabar.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Fira Ministan India Narendra Modi, a birnin New Delhi a ranar Asabar. REUTERS/Cathal McNaughton
Talla

Daga cikin yajejeniyoyin akwai sa hannu wajen karfafa alakar samar da tsaro a mashigin tekun India, da kuma fannonin kasuwanci da zuba hannun jari da jimmilar kudinsu ya kai euro biliyan 13.

Macron ya ce babban makasudin ziyararsa shi ne daukar India a matsayin babbar kawa Faransa a kudancin nahiyar Asiya, da kuma aiki tare akan batutuwan da suka shafi tsaro, canjin yanayi da kasuwanci.

Shugabannin sun kuma amince da hadin gwiwa wajen bunkasa samarwa da kuma sarrafa makamashi daga fannonin hasken rana da gina cibiyoyin makamashin nukiliya.

Zuwa yanzu an shafe akalla shekaru 20 Faransa da India na rike da kyakkyawar alaka ta Dilomasiyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.