Isa ga babban shafi
Syria

"Al'ummar Syria suna fuskantar bala'i fiye da koyaushe"

Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan ne mafi munin lokaci da fararen hula ke shan bakar wahala a yakin basasar Syria da ke shirin shiga shekaru 8 da farawa.

Wani sashi na yankin gabashin Ghouta da jiragen Syria ke ci gaba da yi wa luguden wuta.
Wani sashi na yankin gabashin Ghouta da jiragen Syria ke ci gaba da yi wa luguden wuta. ©REUTERS/ Bassam Khabieh
Talla

Bayanan majalisar dinkin duniyar na zuwa a dai dai lokacin da ayarin motocin agaji suka samu damar shiga wasu yankunan gabshin Ghouta da luguden wutar sojin gwamnatin ya hallaka fiye da mutane 900.

Filippo Grandi shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce fiye da kashi 69% na al’ummar Syria na cikin tsananin wahala a dai dai lokacin da adadin mutanen da suka rasa rayukansu a dalilin yakin basasar kasar ya haura dubu 340,000.

Mista Grandi ya kara da cewa, wannan ne karon farko da aka samu yawaitar ‘yan gudun hijira tun bayan yakin duniya na 2, domin kuwa akalla ‘yan kasar Syria miliyan 20 suka fantsamu zuwa kasashen duniya.

Kalaman na Mr Grandi na zuwa adai dai lokacin da ayarin motocin agaji na Majalisar Dinkin Duniya hade da tarin jami’an lafiya na kungiyar agaji ta kasa da kasa suka samu damar shiga wasu sassa na Syrian, duk da cewa har yanzu, dakarun sojin gwamnatin dana kawancenta basu dakatar da luguden wutar da suke a yankin gabashin Ghouta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.