Isa ga babban shafi
Syria

Amurka da Rasha sun tafka laifukan yaki a Syria - MDD

Tawagar masu sa ido akan yakin Syria ta Majalisar Dinkin Duniya ta zargi kasashen Rasha da Amurka, da hallaka fararen hula masu yawan gaske a Syria, a jerin hare-haren da suka kaddamar kan bangarorin da suke yaka a 2017.

Wani asibiti da ke farmakin jiragen yaki ya rusa a garin Atareb da ke karkashin 'yan tawaye, a yammacin birnin Aleppo.
Wani asibiti da ke farmakin jiragen yaki ya rusa a garin Atareb da ke karkashin 'yan tawaye, a yammacin birnin Aleppo. Ammar Abdullah / Reuters
Talla

Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar, ya kuma zargi gwamnatin shugaban kasar at Syria Bashar al-Assad da kai wa yankunan ‘yan tawaye hare-hare da makamai masu guba, musamman a yankin Gabashin Ghouta, lamarin da ya yi sanadin hallakar daruruwan fararen hula.

Daga cikin misalan da rahoton ya bayyana akwai harin da wani jirgin yakin Rasha ya kai kan wata kasuwa da ke Atareb a yammacin birnin Aleppo cikin watan Nuwamba na 2017, inda fararen hula 84 suka hallaka.

Rahoton ya ce an kai wa yankin farmaki ne duk da cewa kasashen Rasha, Iran da kuma Amurka, sun amince da killace yankin na yammacin Aleppo daga kai hare-hare.

Rahoton ya kara da cewa a watan Maris na shekarar 2017, Amurka ta jagpranci farmakin da aka hallaka fararen hula 150 a wata makaranta da ke gaf da birnin Raqqa, bisa da’awar cewa sun kai wa mayakan IS farmaki ne.

Sai dai bayan gudanar da bincike, tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta bankado cewar, babu alamar akwai mayakan IS da suke wajen, dan haka Amurka ta sabawa dokar kasa da kasa, saboda gazawarta wajen kare rayukan fararen hula a yakin kasar ta Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.