Isa ga babban shafi
Syria

Yawan wadanda suka hallaka a gabashin Ghouta ya zarta 670

Jami’an agaji a Syria, sun ce zuwa yanzu hare-haren da jiragen yakin sojin kasar ke ci gaba da kai wa kan yankin Gabashin Ghouta ya hallaka sama da fararen hula 674 acikin mako guda.

Wani yanki na gabashin Ghouta, da barin wutar jiragen yaki ya ragargaza.
Wani yanki na gabashin Ghouta, da barin wutar jiragen yaki ya ragargaza. REUTERS/Bassam Khabieh
Talla

Farmakin kan yankin ‘yan tawayen na ci gaba da gudana ne, duk da cewa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri’ar tsagaita wutar yakin Syria a ilahirin kasar tsawon kwanaki 30.

Daga cikin fararen hular da suka hallaka akwai kananan yara 22 da mata 43.

A wani labarin kuma, fararen hular da ke zaune a yankin sun ki amincewa da tayin ficewa da gabashin na Ghouta, a karkashin tsarin tgaita wuta a tsawon awanni 5 a kullum da Rasha ta gabatar.

Fararen hular sun bayyana dalilinsu da cewa basu da tabbacin tsare rayukansu a lokacin da suka amsa tayin ficewa daga yankin.

Yankin Gabashin Ghouta mai yawan al’umma dubu 400,000, ya kasance a karkashin kawanyar sojin gwamnatin Syria tun a shekarar 2013, bayan kwace ikon yankin da ‘yan tawaye suka a tsakiyar shekarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.